Gwamnan jihar Zamfara Dakta Bello Matawalle, ya ce duk wani mai rike da mukamin saurata a fadin jihar Zamfara, idan bai kawo karshen kashe-kashe da dauke-dauke da ake yi a yankunan shi ba zai tsige shi a cikin kankanin lokaci.
Matawalle ya bayyana haka ne, yayin wata zantawa da ya yi da manema labarai, inda ya ce su na da rahotannin da su ka tabbatar masu cewa gwamnatin da ta gabata ta daukin ‘yan sintirin sa-kai a kowace karamar hukuma a karkashin jagorancin sarakunan yankunan.
Don haka ya ce idan aka yi wani abu a yankunan, ya kamata a ce sarakunan sun san wadanda su ka aikata, hakan ya sa su ka fito da shirin tsige duk wanda bai kawo karshen matsalar a yankin shi ba.
Ya ce ko a ‘yan makonnin baya sun je wata karamar hukuma, inda mutanen yankin su ka nemi a bar su su kashe sarkin su, bisa zargin ya na da hannu a irin rashin adalcin da ake yi wa makiyaya a yankin na kwace masu dukiyoyi.
You must log in to post a comment.