Home Labaru Rikicin Zabe: INEC Ta Soke Zaben Wani Gari A Jihar Bayelsa

Rikicin Zabe: INEC Ta Soke Zaben Wani Gari A Jihar Bayelsa

480
0

Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta soke zabe mazabar Ologi da ke karamar hukumar Ogbi ta jihar Bayelsa, sakamakon barkewar rikici a yankin da ya hada da sace wani jami’in zabe.

Kwamishinan zabe na karamar hukumar Ogbia Ukuachukwu Orji, ya ce al’ummar garin Ologi sun hana zabe karfi da yaji kamar yadda rahotanni su ka ruwaito.

Ya ce a lokacin da ma’aikatan zabe ke shiga garin bayan sun tsallaka rafi, sun kama su sannan su ka kwace kayayyakin zaben su ka kona.

Jami’in ya cigaba da cewa, sun kori wasu daga cikin ma’aikatan, sun kuma rike wasu amma daga bisani sojoji sun ceto su.Ya ce rikicin da al’ummar garin su ka tada ne sanadiyar soke zaben don gudun tabarbarewar tsaro.

Leave a Reply