Jami’an tsaron kasar Sudan na kokarin tabbatar da ikon su a babban birnin Khartoum bayan hallaka sama da farar hula 100, wadanda ba su dauke da wani makami yayin tarwatsa masu zanga-zangar tabbatar da dimokradiyya.
Kungiyoyi masu adawa na cewa an samu karin mutanen da aka jefa a cikin wani kogi.
An tsinkayi dakarun wata kungiyar mayakan sa-kai ta gwamnati da ake jin tsoron su, su na ta sintiri a birnin, inda rahotanni ke cewa su na harbi da bugu da kuma kama fararen hula.
Haka kuma, ana ganin a ‘yan kawanaki kadan da su ka gabata, ‘yan hamayyar na Sudan ke dab da cimma yarjejeniya da sojojin da ke rikon-kwarya na kasar a kan kafa gwamnatin farar-hula, amma kwatsam al’amurra su ka tabarbare.
Dakaru masu alaka da gwamnati da ke tarwatsa masu zanga-zangar da su ka yi zaman dirshan dai, sun yi nasarar korar wasu fararen hula, lamarin da ya kai ga sun bar dandalin da su ka mamaye zuwa cikin unguwanni.
You must log in to post a comment.