Home Labaru Rikicin Siyasa: APC Ta Bukaci Kotu Ta Yi Watsi Da Karar Atiku...

Rikicin Siyasa: APC Ta Bukaci Kotu Ta Yi Watsi Da Karar Atiku Saboda Ba Dan Nijeriya Ba Ne

331
0

Jam’iyyar APC ta bukaci kotun zaben shugaban kasa da ta yi watsi da karar dan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya shigar domin kalubalantar nasarar da shugaba Muhammadu Buhari ya yi.

APC ta bayyana wa kotu cewa, ta mika wannan bukata ne saboda Atiku Abubakar ba asalin dan Nijeriya ba ne.

Idan dai ba a manta ba, Atiku Abubakar ya yi takarar kujerar shugaban kasa a zaben shekara ta 2019 wanda ya gudana a ranar 23 ga watan Febrairu karkashin inuwar jam’iyyar PDP.

Lauyan jam’iyyar APC Lateef Fagbemi, ya bukaci kotu da yi watsi da wannan kara yayin da ya ke maida martani a kan jawaban da lauyan PDP ya yi na bukatar a soke bukatun jam’iyyar APC.

Fagbemi ya bukaci alkalin kotun ya yi watsi da karar, saboda rashin gamsuwar sa a kan cancantar takarar Atiku Abubakar, tare da bada isassun hujjoji a a kan haka.

APC ta ce, tun farko Atiku bai cancanci yin takara ba, saboda haka ta ke bukatar kotu tayi watsi da bukatar PDP ganin cewa, Atiku Abubakar ba haifaffan Nijeriya ba ne.

Sai dai, lauyan Atiku Chris Uche ya yi jayayya a kan kalaman lauyan APC, inda ya ce tarihi ya tabbatar da cewa Atiku dan Nijeriya ne, saboda haka kada kotu ta yi amfani da haujjojin da APC ta bayar.

Leave a Reply