Wasu matasa sun ƙone wani ɓangare na ofishin sanata Barau Jibrin a Kano, jigo a ɓangaren APC da ya raba gari da ɓangaren gwamnan jihar.
Shaidu sun bayyanawa BBC cewar matasan sun fi 100 da suka abka wa ofishin jam’iyyar.
Wannan na zuwa a yayin da wata kotu a Abuja ta rushe shugabancin ɓangaren gwamna Ganduje tare da tabbatar da jagorancin ɓangaren Shekarau.
Rikicin siyasar APC a Kano na ci gaba da ɗaukar hankali tun bayan gudanar da zaɓen shugabannin jam’iyyar ɓangare biyu, inda wasu ke ganin rabuwar kai a Kano wata babbar ɓaraka ce ga APC.