Daya daga cikin ‘yan Kwamitin Yada Labarai da Kafofin Sadarwa na majalisar dattawa Sanata Betty Apiafi, ta ce bukatar da mabiya akidar Shi’a ke yi ta a saki Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ta fi karfin hurumin Majalisar Dattawa.
Sanatan ta bayyana haka ne, yayin da ‘yan kwamitin su ka yi wa manema labarai bayani a harabar Majalisar da ke Abuja.
Tawagar Sanatocin, a karkashin jagorancin Shugaban Kwamitin Sanata Adebayo Adeyeye, sun yi bayanin ne biyo bayan hargitsin da ya faru a lokacin da ‘yan shi’a su ka kutsa cikin Majalisa da karfin tuwo.
Mabiya Ibrahim El-Zakzakky dai sun yi zanga-zanga a kofar shiga Majalisar dattawa, lamarin da a karshe ya yi muni har aka yi wa wasu jina-jina.
Sanata Adeyeye, ya ce masu zanga-zangar sun ci karfin jami’an tsaron da ke tsare kofar shiga Majalisar, ya na mai yin kira da a kama duk wadanda ke da hannu wajen gudanar da hargitsin da ya faru, a kuma kara yawan jami’an tsaro a Majalisa. �2}s82�