Babbar kotun Kaduna da ke sauraren bukatar neman belin shugaban kungiyar shi’a Malam Ibrahim Elzakzaky da mai dakin sa, ta dage sauraren karar zuwa ranar 5 ga watan Agusta domin yanke hukunci.
Yayin zaman kotun, lauyan El-Zakzaky Femi Falana ya shaida wa kotun cewa, mutumin da ya ke karewa ya na cikin matsanancin halin rashin lafiyar, wanda ke bukatar a fitar da shi kasar waje domin nema masa magani.

Ya ce a kasar waje ne kawai za a iya duba Sheikh Ibrahim El-Zakzaky yadda ya kamata saboda tsanantar da cutar ta yi.
Sai dai lauyan gwamnati Debris Bayero ya soki uzurin da Femi Falana ya gabatar a gaban kotun, inda ya ce ba sai an fitar da El-Zakzakky kasar waje ba, kasnacewar akwai kwararrun likitocin da za su iya duba shi a cikin gida.
You must log in to post a comment.