Home Home Rikicin Rasha Da Ukraine: Amurka Ta Gargaɗi ‘Yan Ƙasarta Su Guji Shiga...

Rikicin Rasha Da Ukraine: Amurka Ta Gargaɗi ‘Yan Ƙasarta Su Guji Shiga Rasha

145
0

Ma’aikatar cikin gidan Amurka ta gargaɗi ‘yan kasar kar su kuskura su yi balaguro zuwa Rasha saboda abin da ta kira shirin Rashar na ɗaukar matakan soji da mamaye Ukraine.

Ma’aikatar ta ce ba lallai ne ofishin jakadandin Amurka a Moscow ya ba su taimakon da suke buƙata ba idan lamura suka lalace.

Haka kuma sun aike da irin wannan gargaɗi ga jami’ansu da ke Ukraine,

Tuni aka ba da umarni ga ma’aikata Amurkawa da iyalan ma’aikatan diflomasiyya su gaggauta ficewa daga Kiv babban birnin Ukraine.

Kazalika jami’ai sun bai wa Amurkawa mazauna Ukraine shawarar su tattara su koma gida tun kafin jirage su fara karanci