Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya ce shugaban jam’iyyar APC ta kasa, Adams Oshiomhole, na shirin jefa tsarin zaman lafiyar siyasar jihar cikin hatsari.
Karanta Wannan: DPR Ta Garkame Gidajen Man Fetur 53 A Jihar Kaduna
Gwamnan jihar ya bayyana hakan ne ta bakin mai magana da yawaunsa Ladan Salihu, inda ya ce gwamnatin jihar ta magance rikicin da ke faruwa a majalisar dokokin jihar.
A wani jawabi da gwamnan ya yi, ya daura laifin rikicin da ya kunno kai a majalisar dokokin jihar akan shugaban jam’iyyar APC ta kasa, Adams Oshiomhole, bayan ya nemi a sake rantsar da majalisar dokokin jihar.
Ladan Salihu, ya ce ‘yan majalisar guda 8 a karkashin jagorancin shugaban APC na kasa na daga cikin mutane 17 da aka rantsar a makon da ya gabata a zauren majalisar.
Gwamnan Bala Mohammed, ya ce wadanda suka jagorancin wata kungiyar sasanta rikicin majalisar dokokin jihar ne, suka rage bayanan da shugaban kasa ya yi, akan rikicin saboda son ransu.
Daga karshen Gwamnatin jihra ta ce ita da mutanen ta, sun san cewa duk wani rikici a majalisar ya zama tarihi, saboda sun zama tsintsiya madaurinki daya.