Tsohon gwamnan jihar Sokoto Alhaji Dalhatu Attahiru Bafarawa, ya soki lamirin manyan arewa, dangane da yin shiru a kan rikicin masarautar Kano, inda ya ce hakan na iya zama matsala ga daukacin kasar nan baki daya.
Bafarawa ya ce, rikicin ba rikicin jihar Kano ba ne kawai, rikici ne na yankin arewa baki daya, kuma abin da ya shafi yankin arewa tamkar ya shafi kasa ne baki daya.
Ya ce bai dace a ce irin wadannan mutane sun samu rikici a junan su, amma babu wani babban mutum daga cikin dattawan arewa da zai yi masu magana, duk da cewa arewa ke da Sarkin Musulmi, ga kuma Sarkin Zazzau da Shehun Borno da manyan sarakuna da malamai.
Bafarawa ya kara da cewa, abin kunya ne a ce dan yankin kudu kamar gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi ne zai zo ya yi sulhu tsakanin gwamnan Kano da Sarkin Kano.
Ya ce kamata ya yi manyan arewa su hada kwamitin da zai kunshi dattawan arewa da sarakuna da malamai da ‘yan kasuwa, kuma shi kan sa shugaba Muhammadu Buhari bai dace a ce ya na kallo hakan ta na faruwa a yankin shi ba.