Home Labaru Rikicin Kabilanci: ‘Yan Sanda Sun Kama Mutane 7 Da Ake Zargi Da...

Rikicin Kabilanci: ‘Yan Sanda Sun Kama Mutane 7 Da Ake Zargi Da Haddasa Rikici A Kwara

371
0

Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta ce ta kama mutane 7 da ta
ke zargi da hannu a hargitsin da ya faru a tsakanin wasu
al’umomi da ke jihar Kwara.
Kakakin rundunar jihar Ajayi Okasanmi ya tabbatar da kamen
wadanda ake zargin a lokacin da ya ke tattaunawa da manema
labarai ta wayar tarho a ranar Talatar da ta gabata.
Okasanmi ya kuma tabbatar da cewa, an kashe mutum guda a
yayin da aka jikkata wasu da dama a lokacin rikicin, wanda ya
barke a tsakanin al’umomin a ranar Lahadi, sakamakon wani
sabani da ya abku da su a lokacin da su ke gudanar da
bukukuwan dodonni a yankin.
A nashi bangaran, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kayode
Egbetokun ya bada umurnin kama daukacin masu hannu a
rikicin tare da hukunta su.

Leave a Reply