Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Rikicin Jam’iyyar APC Na Cigaba Da Tazzara

Oshiomhole Ya Jinjinawa Buhari Bisa Rage Kudin Man Fetur

Adams Oshiomhole, Shugaban Jam’iyyar APC Ta Kasa

Rikicin cikin gida na ci-gaba da ta’azzara a jam’iyyar APC, inda wasu jiga-jigan jam’iyyar ke ganin ya kamata shugaban ta na kasa Adams Oshiomhole ya sauka daga mukamin sa don a samu zaman lafiya.

Rikicin da ake ganin tamkar ‘yan jam’iyyar adawa ne ke yada jijta-jita akai, yanzu haka ya fara bayyana a fili, inda rashin jituwa tsakanin Oshiomole da wasu ‘yan jam’iyyar a jihohi ya bayyana.

Da dama daga ‘yan jam’iyyar APC na ganin hanya daya da za a iya dinke barakar ita ce Adams Oshiomole ya sauka daga mukamin sa.

Mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa reshen a arewacin Nijeriya Sanata Lawal Shu’aibu, ya ce shugabannin jam’iyyar na jihohi sun ce ba su yarda ba sai Oshiomole ya sauka.

Ya ce babu yadda za a yi jam’iyya ta cigaba a haka saboda irin rabuwar kawunan da ke jam’iyyar ba abu ne da za a iya dinkewa cikin sauki ba.

Exit mobile version