Wata sabuwar rigima ta kunno kai a jam’iyyar APC reshen jihar Katsina, sanadiyyar sakamakon zaben dan takarar kujerar gwamnan jihar.
Wata majiya ta ruwaito cewa, Dakta Mustapha Inuwa ya fara babatu bayan ya rasa tikitin takarar kujerar gwamnan.
Mustapha Inuwa, wanda ya sauka daga kujerar Sakataren gwamnatin jihar domin tsayawa takarar, ya zargi ‘yan jam’iyyar APC da cin amanar sa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, Mustapha Inuwa ya yi alkawarin taimaka wa yaran sa da su ka koma jam’iyyar NNPP.
Wadanda su ka sauya-shekar zuwa jam’iyyar NNPP dai su na zargin ba a yi masu adalci ba, lamarin da ake ganin zai iya zama barazana ga jam’iyyar APC.
Dr. Mustapha Inuwa, ya ce an ki ba shi damar ya tsaya takarar ne domin ba za a iya juya shi ba, don haka aka zabi wanda bai san komai ba.