Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta harba rokoki kimanin 100 a kan yankunan kungiyar mayakan Hezbollah a kudancin Lebanon, a matsayin martani na wasu makaman roka da ‘yan kungiyar ta Shi’a suka harba cikin arewacin Isra’ila ranar Asabar da yamma.
Hezbollah ta ce mayakanta sun lalata wata motar sojoji, yayin da Isra’ilar ta ce ba wanda ya jikkata a sanadiyyar hare-haren kungiyar ta Lebanon.
Kamar yadda rundunar sojin kasa ta Isra’ilar ta sanar, ta ce, an harba wasu ‘yan makaman roka masu tarwatsa igwa-igwa kan wani sansanin soji da kuma kan wasu motocin yaki nata, daga kasar Lebanon.
Kasar ta ce saboda haka ne ita ma ta mayar da martani da makamai masu linzami da jiragen yaki masu saukar ungulu, inda ta harba makaman atilari kusan 100, zuwa sansanonin mayakan Hezbollah a cikin Lebanon.
Duk da cewa Hezbollah ta yi ikirarin cewa ta tarwatsa wata igwa ta sojin Israila, da kashe sojoji da dama, Firaministan Isra’ilar Benjamin Netanyahu, ya ce sam-sam ba wani da ya jikkata daga bangarensu, hasali ma ko kwarzane ba wanda ya yi, in ji shi.