Home Labaru Rikici: An Kashe Mutane Uku Da Shanu 319 A Jihar Filato

Rikici: An Kashe Mutane Uku Da Shanu 319 A Jihar Filato

862
0

Rundunar ‘yan Sanda ta Jihar Filato, ta tabbatar da kashe mutane uku da shanu masu yawa a wani sabon rikici da ya barke a Karamar Hukumar Bassa.

Kakakin rundunar ‘yan Sanda na jihar Tyopev Terna, ya ce an yi kashe-kashen ne a kauyukan Billi da Ariri.

Ya ce an kashe shanu 319 kwana daya bayan an kashe mutane uku, tare da ji ma wani rauni a Miyango da Rotsu, wadanda kauyuka ne duk a cikin Karamar Hukumar Bassa.

A cikin wata sanarwar da ya raba wa manema labarai, Terna ya ce wasu makiyaya biyu da su ka hada da wani Mubarak Yakubu da Shehu Saidu sun bace, har yau ba a san inda su ke ba.

Ya ce sun samu rahoton kai harin da aka kashe mutane uku a ranar 29 ga watan Afrilu, sai kuma ranar 30 ga watan su ka sake samun rahoton kashe shanu 319 tare da sace wasu 11.

Kakakin ya cigaba da cewa, ’yan sanda sun shiga neman wadanda su ka bace, kuma ana kokarin kamo wadanda duk ke da hannu a wadannan kashe-kashe.

Leave a Reply