Home Labaru Rikice-Rikice: An Kai Hari Kan Kabilar Jukun A Taraba

Rikice-Rikice: An Kai Hari Kan Kabilar Jukun A Taraba

709
0

Mutane shida ne suka mutu ciki hadda wata tsohuwa, a wani hari da wasu ‘yan ta’adda suka kai garin Tsondi dake karamar hukumar Wukari jihar Taraba.

Maharan sun shiga kauyen ne da asubar fari inda suka harbe mutane masu yawan gaske.

Rahotonni na cewa mutane shida ne suka mutu a lokacin da aka kai harin sannan kuma wasu da dama suka jikkata.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun fito ne daga jihar Binuwai, wacce ke makwabtaka da jihar ta Taraba inda suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi.

Bayan haka kuma maharan sun sanyawa gidaje da yawan gaske wuta, inda suka tilastawa al’ummar garin yin hijira suna komawa cikin garin Wukari da wasu kauyuka da suke makwabtaka da su domin tsira da rayukan su.

Leave a Reply