Home Labaru Rigar Kowa: Allah Ya Yi Wa Dakta Ibrahim Yakubu Lame Rasuwa A...

Rigar Kowa: Allah Ya Yi Wa Dakta Ibrahim Yakubu Lame Rasuwa A Abuja

399
0

An sanar da mutuwar Dakta Ibrahim Yakubu Lame jigo kuma dan takarar gwamnan jihar Bauchi a karkashin jam’iyyar APC a zaben shekara ta 2019.

Dakta Lame ya taba rike mukamin minista mai kula da harkokin rundunar ‘yan sanda, sannan ya na rike da sarautar ‘San-Turakin Bauchi.

Dan siyasar ya rasu ne da sanyin safiyar Lahadin nan, a asibitin Nizamiye da ke Abuja, bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Tuni dai aka sallaci gawar sa da misalin karfe 10:00 a babban masallacin kasa da ke Abuja.

An haifi Marigayi Lame, malami kuma dan siyasa a shekara ta 1953, sannan an zabe shi a matsayin sanata a shekara ta 1992 a jamhuriya ta uku.

Marigayin ya taba rike mukamin mai ba tsohon shugaban kasa Obasanjo shawara a shekara ta 1999, kafin daga bisani marigayi Umaru Musa Yar’adua ya nada shi minista a shekara ta 2008.

Leave a Reply