Home Labaru Kiwon Lafiya Riga-Kafi: Nijeriya Ta Yi Shirin Ko-Ta-Kwana A Kan Cutar Ebola

Riga-Kafi: Nijeriya Ta Yi Shirin Ko-Ta-Kwana A Kan Cutar Ebola

420
0

Ma’aikatan lafiyan da aka tura kan iyakar Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo da Uganda a bakin aiki

Nijeriya ta ce ta bullo da wasu matakai don shirin ko-ta-kwana a kan cutar Ebola, wadda ke kara bazuwa tun bayan barkewar ta a Jamhuriyar Dimokradiyya Kongo da kuma Angola a baya-bayan nan.

Cibiyar takaita yaduwar cututtuka ta ce, kwamitin shirin tunkarar cutar Ebola a Nijeriya ya dauki matakai da dama ciki har da tabbatar da ganin cibiyar kai daukin gaugawa ta kasa ta na aiki kuma yanzu haka ta na cikin shirin ko-ta-kwana.

Cibiyar takaita yaduwar cututtuka ta ce, matakan sun zo ne sakamakon aikin tantance hatsarin bazuwar cutar Ebola daga kasashen Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo da Uganda zuwa Nijeriya.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar 11 ga wannan Yuni ne ma’aikatar lafiya ta kasar Uganda ta tabbatar da bullar cutar a lardin Kasese kusa da kan iyakar Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo.

Leave a Reply