Home Labaru Ricikin Kabilanci: Rayuka 12 Sun Salwanta A Birnin Abakaliki Na Jihar Ebonyi

Ricikin Kabilanci: Rayuka 12 Sun Salwanta A Birnin Abakaliki Na Jihar Ebonyi

322
0

Kimanin rayukan Mutane 12 sun salwanta, yayin wani mummunan rikicin kabilanci da ya barke a birnin Abakaliki na jihar Ebonyi.

Rikicin, wanda ya barke ne tsakanin kabilar Eyigba ta karamar hukumar Izzi da kabilar Eyibuchiri ta karamar hukumar Ikwo, ya salwantar da rayukan Mutane 12 kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Lamarin dai ya faru ne a ranar Asabar da ta gabata, inda wadanda abin ya rutsa da su, su ka gamu da ajalin su a kan hanyar su ta dawowa daga bikin murnar shigar sabbin daliban jami’ar Ebonyi.

Rahotanni sun ce, an yi wa Matafiyan kwanton bauna daura da hanyar jami’ar tarayya ta Alex Ekueme, inda aka kone su kurmus a cikin motar da ke dauke da su.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Ebonyi DSP Loveth Odah ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni kwamishinan ‘yan sanda na jihar Awosola Awotunde ya kai ziyarar gani da ido a yankin da rikicin ya faru.