Mai ba shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro Nuhu Ribaɗu,
ya bukaci rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta haɗa hannu da
sauran hukumomin tsaro domin samun nasarar kauda matsalar
rashin tsaro a Nijeriya.
Nuhu Ribadu ya bayyana haka ne, lokacin da yake tattaunawa da shugaban ‘yan sandan Nijeriya Adeolu Egbetokun yayin da ya kai masa ziyara ofishin sa da ke Abuja.
Shugaban ‘yan sandan, ya ce ziyara ce ta musamman ya kai wa Nuhu Ribadu domin taya shi murna a kan mukamin da ya samu da kuma tattauna harkar tsaron kasa.
Nuhu Ribadu, ya ce matakan da shugaban ‘yan sandan ya fara aiwatarwa tun bayan nada shi ya nuna cewa lallai da gaske aikin ya zo ya yi ba wasa ba.