Home Home Remi Tinubu Ta Sanya Wa Babban Dakin Taron Cibiyar Mata Ta Abuja...

Remi Tinubu Ta Sanya Wa Babban Dakin Taron Cibiyar Mata Ta Abuja Sunan Maryam Abacha

93
0

Uwargidan shugaban kasa Oluremi Tinubu, ta sauya sunan babban dakin taro na ‘Maryam Babangida zuwa sunan Maryam Abacha.

Zauren, wanda a da ake kira da ‘African Peace Mission Hall’,  a Turance, uwargidan shugaban kasar ce ta kaddamar da shi kuma aka canza ma shi suna zuwa Maryam Abacha, saboda irin gudummawar da ta bada wajen samar da zaman lafiya a nahiyar Afrika.

Sanata Oluremi Tinubu, ta ce taron muhimmi ne a kokarin hadin gwiwa wajen karfafa alaka tare da bunkasa ci-gaban da aka samu wajen samun hadin kai da dawwamammiyar dangantaka a tsakanin mata.

Haka kuma, ta bayyana Maryam Abacha a matsayin mace mai hazaka kuma jajirtacciya wajen ci-gaban nahiyar Afrika baki daya.

A nata bangaren, Dakta Maryam Abacha ta yi wa Nijeriya da gwamnatin shugaba Tinubu da mataimakin sa Kashim Shettima addu’a a kan Allah ya ba su ikon cimma nasara.

Leave a Reply