Home Labarai Rayuwata Na Cikin Hadari – Kwamishinan Inec a Adamawa

Rayuwata Na Cikin Hadari – Kwamishinan Inec a Adamawa

83
0

Kwamishinan hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa a jihar
Adamawa Barista Hudu Yunusa Ari, ya yi zargin cewa
rayuwar sa ta na cikin hadari.

Hudu Ari ya bayyana haka ne, lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a gidan sa dake Bauchi, inda ya bada tabbacin duk da rayuwar sa ta na cikin hadari, hukumar zabe za ta gudanar da karbabben zabe bisa gaskiya da adalci.

Ya ce a matsayin shi na kwamishinan hukumar zabe ba ya tare da kowace jam’iyya ko dan takara, dukkan su daya su ke a wajen sa, don haka ba ya da wani dalilin kin wani ko goyon bayan wani dan takara ko jam’iyya.

A karshe ya yi Allah-Wadai da barazanar da ake yi wa lafiyar sa, ya na mai jaddada cewa a shirye ya ke ya aiwatar da duk umurnin da helkwatar hukumar zabe ta ba shi.

Leave a Reply