Home Labaru Rashin Tsaro: Za Mu Kori Batagarin Fulani Daga Yankin Yarabawa – Ooni...

Rashin Tsaro: Za Mu Kori Batagarin Fulani Daga Yankin Yarabawa – Ooni Na Ife

387
0

Babban basaraken kasar Yarabawa Ooni na Ife Adeyeye Ogunwusi, ya ce su na shirye-shiryen fatattakar duk wasu batagarin Fulani makiyaya daga yankin Yarabawa baki daya.

Basaraken ya bayyana haka ne, a lokacin da ya karbi bakuncin Sarkin Borgu Muhammad Dantoro, inda ya koka da yawan hare-haren da ya ce ana kaiwa a yankin, ya na mai cewa a baya ba su san da irin wadannan hare-hare a yankunan su ba.

A cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai, kakakin yada labarai na Fadar Ooni na Ife Moses Olafare, ya ce basaraken ya ce su na zaune da Fulani a yankunan su, amma wasu batagari daga cikin su su na neman mamaye su, don haka ya ce za su fatattake su domin samar da zaman lafiya a yankin.

Ya ce yanzu lokaci ya yi da za a tantance tsaki da tsakuwa, wato a tantance tsakanin Fulani masu son zaman lafiya da kuma batagarin cikin su.

Leave a Reply