Home Labaru Rashin Tsaro: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 18 A Jihar Sokoto

Rashin Tsaro: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 18 A Jihar Sokoto

359
0

Rahotanni daga jihar Sokoto na cewa, a kalla mutane 18 sun rasa rayukan su, bayan wasu ‘yan bindiga sun afka wa wani kauye da ke gabashin jihar a ranar Litinin da ta gabata da daddare.

Wani basarake da yankin ya shaida wa manema labarai cewa, lamarin ya faru ne a kauyen Malafaru da ke karamar hukumar Goronyo.

Harin dai ya zo ne, makonni kadan bayan wasu ‘yan bindiga sun hallaka mutane da dama a yankin karamar hukumar Rabah.

Jihar Sokoto dai ta na iyaka da jihar Zamfara, inda barayin shanu da masu garkuwa da mutane su ka hallaka dubban mutane tun daga shekara ta 2011.

Leave a Reply