Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Rashin Tsaro: Mun Taba Yi Wa Mutum 76 Jana’Iza A Lokaci Guda, Babu Wanda Ya Ji Labari Inji Sulta

Sultan-of-Sokoto

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, yace ba a bada cikakken labari a kan irin kashe-kashen da ake fama da shi a yau.

Da yake jawabi a wajen taron majalisar addinai na kasa a birnin tarayya Abuja, an ruwaito cewa Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar III yana cewa sha’anin rashin tsaro ya yi kamari a naijeriya, ya kuma yi alkawarin cigaba da fadin gaskiya har sai an shawo kan lamarin.

Mai alfarma Sarkin Musulmin ya bayyana cewa dole a bankado mutanen da suke yin wannan danyen aiki, domin a yanke masu hukuncin da ya dace.

Wata jarida ta ruwaito cewa Sultan yana zargin shugabannin al’umma da ‘yan siyasa da yin kalaman kiyayya da za su iya jawo a rika kashe mutane ba da dalili ba.

Exit mobile version