Home Labaru Rashin Tsaro: Matasa Sun Kona Gidan Kwamishinan Tsaro Da Na Basarake A...

Rashin Tsaro: Matasa Sun Kona Gidan Kwamishinan Tsaro Da Na Basarake A Jihar Sokoto

216
0

Wata zanga-zangar nuna damuwa a kan ta’azzarar matsalar tsaro a garin Isa da ke jihar Sokoto ta rikide zuwa tarzoma, lamarin da ya yi sanadiyyar kona gidajen kwamishinan tsaro da na sarkin garin.

Karamar hukumar Isa dai ta na daya daga cikin yankunan da su
ka dade su na fama da matsalar ‘yan bindiga, lamarin ya kara
ta’azzara sakamakon fatattakar da sojoji ke yi wa ‘yan bindiga a
dajin Zamfara.

Tuni dai lamarin ya sa matasa su ka gudanar da zanga-zanga
domin nuna fushin su, sai dai daga bisani zanga-zangar ta dauki
sabon salo, inda wani bangare na masu zanga-zangar su ka kai
hari tare da kona gidajen kwamishinan tsaro na jihar Kanar
Garba Moyi mai murabus, da kuma na sarkin Gobir duk a cikin
garin Isa.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Sokoto ASP Sanusi
Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin.

Sarkin Gobir na Isa Nasiru Ahmad na biyu, ya bayyana
mamakin dalilin kai farmaki a gidan sa, duk da kasancewar ba
shi ke rike da ragamar sha’anin tsaro ba.

Leave a Reply