Home Labarai RASHIN TSARO: INEC BA ZA TA GUDANAR DA ZABE A WASU WURARE...

RASHIN TSARO: INEC BA ZA TA GUDANAR DA ZABE A WASU WURARE A NAJERIYA BA

108
0

Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya wato INEC  Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce, ba za ta gudanar da zabe mai zuwa a rumfuna 240 ba.

Farfesa Mahmud Yakubu ya bayyana haka ne a nan Abuja yayin wani taro da jam’iyyun siyasa, ya ce wadannan rumfuna 240 babu wanda ya yi rajistar kada kuri’a a cikin su, domin mutanen yankunan sun warwatsu a sassan jihohin Najeriya 28 da suka hada babban birnin tarayya Abuja.

Shugaban hukumar ta INEC ya ce, hukumar za ta fitar da cikakken jerin sunayen rumfunan zaben da lambobin su da kuma yankunan su a matakin jihohi da kananan hukumomi.

Ya ce akwai rumfunan zabe 34 a jihar Taraba da kuma 38 a jihar Imo da babu wanda ya yi rajistar kada kuri’a a cikin su, yayin da ake da daya zuwa 12 a sauran jihohin da suka hada da nan babbab birnin tarayya Abuja.

Leave a Reply