Home Labaru Rashin Tsaro: Gwamnati Ta Dora Laifin Rikicin Arewa A Kan Sarakunan Gargajiya

Rashin Tsaro: Gwamnati Ta Dora Laifin Rikicin Arewa A Kan Sarakunan Gargajiya

367
0

Ministan Tsaro Mansur Dan Ali, ya ce wasu sabbin bayanan sirri sun nuna cewa, akwai hannun wasu manyan sarakunan gargajiya a kashe-kashen da ake ci-gaba da kaddamarwa a wasu yankuna na arewacin Nijeriya.

Ya ce sun gano cewa, sarakunan gargajiyar da ba a bayyana sunan su ba, su na da hannu a hare-haren ‘yan bindigar, amma ya lashi takocin cewa za su fuskanci hukunci.

Ministan, ya bukaci al’ummar jihohin Zamfara da Katsina da Sokoto da sauran sassan arewacin Nijeriya, su tashi tsaye wajen bada goyon baya ga yunkurin gwamnati na magance tashin hankalin, duba da cewa sojojin da ke filin daga ba za su iya yakar maharan su kadai ba.

Dan Ali ya kara da cewa, tsaida ayyukan hakar ma’adanai da aka yi, ya kasance daga cikin shawarwarin da gwamnatin ta dauka domin tabbatar da kwanciyar hankali a yankin.