Home Addini Rashin Tsaro Da Yunwa: Mun San Mafita Aiwatarwa Ne Matsala —Sarkin Musulmi

Rashin Tsaro Da Yunwa: Mun San Mafita Aiwatarwa Ne Matsala —Sarkin Musulmi

109
0

Mai al’farma sarkin musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na III, ya ce jagororin Arewa sun san hanyoyin da za a magance matsalar tsaro da talauci da yunwa, amma ba su hakan a aikace ba.

Sa’ad Abubakar bayyana haka ne a lokacin taron sarakuna da jagororin Arewa, inda ya jaddada masu cewa matsalar tsaro da rashin aikin yi da talauci da suka addabi yankin babbar barazana ce ga Nijeriya.

Da ya ke jawabin da taron wanda ya gudana a Kaduna, Sa’ad Abubakar ya ce yanzu ’yan Najeriya a fusace suke, saboda yunwa da talauci da durkushewar harkokin samun kudi, saboda haka babu yadda za a yi abubuwa su tafi daidai.

 A nasa jawabin, gwamnan jihbar Kaduna Uba Sani da ya samu wakilcin mataimakiyarsa Hadiza Balarabe, ta ce samar da tsaro babban ginshiki ne wajen ci gaban Arewa.

Haka kuma, shugaban hukumar tsaro na farin kaya DSS Yusuf Magaji Bichi, wanda ya samu wakilcin daraktan hukumar na Kaduna Abdul Enenche a taron, ya jaddada muhimmancin sarakunan gargajiya wajen dakile barazanar tsaro, sannan ya bukaci samun hadin kai wajen yaki da miyagun ayyukana.

Leave a Reply