Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Rashin Tsaro: An Yi Garkuwa Da Jariri Dan Wata Hudu A Akwa Ibom

UNI366331.JPG

UNI366331.JPG

Maharan sun kutsa har cikin uwar dakin ma’aurata suka dora musu bindiga a kai, sannan suka kwace jaririn a akwai IBOM.

Wasu ’yan bindiga biyu suka kutsa cikin gidan wani magidanci mai suna Mista Edeme Eyo suka kwace jaririn nasu.

Mista Edeme Eyo ya ce maharan da suka zo dauke da bindigogi da adduna sun kuta shar cikin uwar dakinsu ne suka dora musu bindiga a kai da matarsa, suka nemi a ba su jaririn.

A cewarsa, ’yan bindigar sun fi karfinsa, matarsa tana ihu, amma suka kwace jaririn daga hannunta suka shiga wata mota da suka zo da ita suka tsere.

Magidancin ya ce wannan abin ya faru ne ba da jimawa ba da ya rasa dansa na fari, wanda ya rasu ’yan watanni bayan haihuwarsa.

Iyayen jaririn da ke zaune a kauyen Enen-Atai da ke Karamar Hukumar Itu sun roki jami’an tsaro su taimaka su ceto musu jaririn nasu daga hannun maharan.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin ’yan sandan Jihar Akwa Ibom, ASP Timfon John, ya ce rundunarsu tana kokarin kamo ’yan bindigar da kuma ceto jaririn don mika shi ga iyayensa.

Exit mobile version