Kungiyar dattawan arewa ta sake sabonta kiran da take yi na
neman Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi murabus.
A lokacin da yake magana da manema labarai, mai magana da
yawun kungiyar Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya ce hujjojin da ke
kasa sun marawa kiraye-kiraye da suke yi ga shugaban kasa ya
yi murabus a baya.
Ya ce shugaban kasa ya yi rantsuwa da Al-Qur’ani domin kare
al’umman Najeriya, amma ya gaza yin hakan, kuma wannan shi
ne shekarar sa ta biyar akan mulki.
Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya kara da cewar halin da ake ciki ya
na kara tabarbarewa a karkashinsa kuma babu alama da ke nuna
abubuwa za su inganta.
Kungiyar ta ce rayuwa a karkashin wannan gwamnati ba ta da
wani tasiri, inda ta ce abinda ake bukata da shugaban da ya rasa
mafita shi ne ya yi murabus.