Home Labaru Rashin Lafiya: An Fitar Da Sabon Gwamnan Jihar Borno Daga Filin Karbar...

Rashin Lafiya: An Fitar Da Sabon Gwamnan Jihar Borno Daga Filin Karbar Rantsuwa

985
0

Ana tsakiyar gudanar da bikin rantsar da sabon gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ne, aka fitar da shi daga farfajiyar taron saboda rashin lafiya da ya ke fama da shi.

Lamarin dai ya faru ne a ranar Larabar nan, yayin da aka rantsar da sabon gwamnan da mataimkain sa Umar Kadafur.

Wata majiya ta ce, sabon gwamna bai kai ga kammala jawabin sa na farko a matsayin gwamna ba aka fitar da shi daga farfajiyar saboda ya gaza magana.

Majiyar ta cigaba da cewa, babban alkalin jihar Borno Kashim Zanna ne ya rantsar da sabon gwamnan a gaban dubunnan al’ummar jihar Borno da shugabanni da manyan jami’an gwamnati.

Tsohon gwamnan jihar Kashim Shettima, ya bayyana farin cikin sa kan mika ragamar mulki ga wanda ya ke kyautata zaton mutumin arziki ne kuma kwararre da zai iya kawo wa jihar Zamfara cigaba.

Leave a Reply