Home Labaru Rashin Inganci: NAFDAC Ta Rufe Kamfanonin Haɗa Magani Shida A Najeriya

Rashin Inganci: NAFDAC Ta Rufe Kamfanonin Haɗa Magani Shida A Najeriya

404
0

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya NAFDAC ta rufe kamfanonin haɗa magani guda shida saboda rashin tsafta a harkokin su.

Mai magana da yawun hukumar, Sayo Akintola, shi ne ya bayyana matakin a madadin shugabar hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye.

Ya ce hukumar ta yi hakan ne bisa haƙƙinta na hana yaɗa kayayyaki marasa inganci a ƙasa baki ɗaya.

Ya ce An rufe kamfanonin ne bayan wani bincike a kan ayyukan su na ƙasa baki ɗaya.

Ya kara da cewa waɗannan kamfanoni duk da irin gargaɗin da aka yi musu, sun gaza bin tsaftataccen tsarin gudanar da ayyuka na GMP domin tabbatar da tsaftar magunguna.

Kazalika, shugabar ta koka kan yadda kamfanonin, waɗanda na cikin gida ne, suka gaza bin ƙa’idoji marasa tsauri na kiyaye tsafta da ingancin kayayyakin su.

Leave a Reply