Kungiyar Ƙwadago ta TUC, ta yi barazanar tafiya yajin aiki matsawar matsalar ƙarancin man fetur ta cigaba nan da ‘yan kwanaki kaɗan masu zuwa.
TUC ta bada sanarwar ne ta bakin Babban Ma’ajin ƙungiyar na ƙasa Mohammad Yunusa, a wajen taron Manyan Jami’an Kamfanoni Masu Zaman Kan Su Da Manyan Jami’an Kamfanonin Gwamnati.
Matsalar ƙarancin mai daita faru ne daga lokacin da aka gano an shigo da gurɓataccen mai ciki Nijeriya, lamarin da ya janyo ƙarancin fetur a gidajen mai.
Duk da cewa kamfanin NNPC ya ce matsalar fetur za ta gushe, kungiyar ƙungiyar ta yi barazanar shiga yajin aiki idan har matsalar ta cigaba a faɗin Nijeriya.