Home Labaru Ilimi Rashin Albashi: Ma’Aikatan Jami’Oi Sun Ƙuduri Shiga Yajin Aiki A Najeriya

Rashin Albashi: Ma’Aikatan Jami’Oi Sun Ƙuduri Shiga Yajin Aiki A Najeriya

75
0

Ƙungiyar manyan ma’aikatan Jami’oin Najeriya, SSANU da kuma ta ma’aikatan jami’a da basa koyarwa, NASU sun ce za su tsunduma yajin aiki a ranar Litinin mai zuwa.

Ƙungiyoyin sun cimma matsayar a ƙarshen wani taron da suka kammala a birnin Akure na jihar Ondo.

Kungiyoyin biyu SSANU da NASU sun ce za su shiga yajin aikin na gargaɗi na kwana bakwai ne domin neman gwamnati ta biya musu wasu haƙƙoƙinsu.

Ciki har da rashin biyan albashinsu na wata 4 da gwamnatin tarayya ba ta yi ba a lokacin da suka shiga yajin aiki na ƙasa baki ɗaya, a shekarar 2022.

Ƙungiyoyin sun nuna rashin jin daɗinsu kan rashin biyan mambobinsu albashin duk kuwa da cewa gwamnatin tarayya ta biya takwarorinsu na malaman jami’oi nasu kuɗaɗen.

Shugaba Bola Tinubu tuni ya bayar da umarnin a biya ma’aikatan jami’oin kuɗaɗensu da aka yi, sai dai ƙungiyoyin na cewa har yanzu basu gani a ƙasa ba.

Leave a Reply