Home Labaru Rashawa: Jam’iyyar PDP Ta Bukaci Shugaba Buhari Ya Yi Murabus

Rashawa: Jam’iyyar PDP Ta Bukaci Shugaba Buhari Ya Yi Murabus

317
0

Jam’iyyar PDP ta bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi murabus saboda zargin rashawa da ake yi a hukumomin tarayya.

Shugaban Jam’iyyar Prince Uche Secondus ya yi wannan kiran, yayin wata hira da ya yi da manema labarai a Abuja

Secondus, ya ambaci binciken rashawar da ake yi a hukumomin NDDC da MIC da NEDC da EFCC da sauran su, inda ya ce da ƙyar Nijeriya ke numfasawa a karkashin mulkin shugaba Buhari. 

Ya ce rashawa ta zama ruwan dare a Nijeriya, yayin da Buhari ke ci-gaba da kauda kan sa, ya na mai ikirarin cewa shugaba Buhari ya yi watsi da alƙawarin da ya yi na yaƙi da cin hanci da rashawa yayin yaƙin neman zaben sa a shekara ta 2015 da 2019.

Leave a Reply