Home Labaru Rantsar Da Tinubu: Za A Kulle Wasu Ma’Aikatu A Abuja Tsawon Kwana...

Rantsar Da Tinubu: Za A Kulle Wasu Ma’Aikatu A Abuja Tsawon Kwana Huɗu

15
0

Hukumomi a Nijeriya za su hana shiga da fita a kewayen
Sakatariyar Gwamnatin Tarayya da ke tsakiyar birnin Abuja
na tsawon kwana huɗu, saboda bikin rantsar da Zaɓaɓɓen
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Haka kuma, jami’an tsaro za su kulle ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya tun daga ranar Juma’a, 26 zuwa Talata, 30 ga watan Mayu.

Wata sanarwa da ofishin kula da ma’aikatan gwamnatin tarayya ya fitar, ta ce ba za a ƙyale ma’aikata da masu ziyara su shiga ma’aikatun ba har sai ranar Talata, 30 ga watan Mayu.

A ranar Litinin, 29 ga watan Mayu ne za a rantsar da Bola Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin shugaban Nijeriya.

Sai dai jam’iyyun PDP da Labour da ‘yan takarar su, su na ƙalubalantar sakamakon zaɓen a kotu cewa an tafka maguɗi.