Shugaba Buhari ya tafi kasar Sanagal, domin halartar kaddamar da shugaban kasar Macky Sall, a bisa sake zaben sa da aka yi a karo na biyu.
Mai ba shugaban kasan shawara a kan harkokin yada labarai, da hulda da jama’a Femi Adesina ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
Ya ce tafiyar ta shugaban kasa Buhari zuwa kasar Sanagal ta biyo bayan gayyatar da Macky Sall ya yi ne.
Sanarwar ta kara da cewa, a matsayin shugaban kasa Buhari, wanda shi ne shugaban kungiyar ECOWAS, zai zama babban bako na musamman a wajen bikin kaddamarwar, wanda sauran shugabannin Afrika za su halarta a ranar Talatar nan.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, wasu gwamnoni da suka hada da Muhammed Abubakar na jihar Bauchi da Nasir El-Rufai na jihar Kaduna Tanko Al-Makura na jihar Nasarawa ne suka yiwa Buhari rakiya zuwa taron kaddamarwar.
Sauran da ke cikin tawagar sun hada da Ministan harkokin kasashen waje Geoffrey Onyeama da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno da babban daraktan hukumar binciken sirri ta kasa Ahmed Rufai, da sauran manyan jami’an gwamnati.
You must log in to post a comment.