Mai al’farmasa Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar na III ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta inganta makarantun tsangaya domin ganin an magance matsalolin barace-barace a kan tituna.
Sa’ad Abubakar ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya ke gabatar da jawabi a wani taron tunawa da ranar ‘yancin kan Nijeriya da ta gudana a Abuja.
Sarkin Musulmin ya ce ya yi imanin cewa, daya daga cikin matakan da za a bi wajen magance matsalar barace-barace shi ne a inganta makarantun tsangaya.
A karshe ya ce, a mafi yawan yaran da suke barace-barace a kan tituna ba su damu da karatun da suka je nema ba, kuma Musulunci bai yarda da bara ba.
You must log in to post a comment.