Home Labaru Ranar Ma’aikata: Gwamnatin Tarayya Ta Sanar Da Laraba A Matsayin Ranar Hutu

Ranar Ma’aikata: Gwamnatin Tarayya Ta Sanar Da Laraba A Matsayin Ranar Hutu

473
0

Gwamnatin tarayya ta sanar da hutun kwana guda ga daukacin ma’aikata domin ba su damar gabatar da bikin murnar ranar ma’aikata.

Ministan harkokin cikin gida Abdulrahman Dambazau ya bayyana haka, a cikin wata sanarwa da babban sakataren ma’aikatar Georgina Ekeoma Ehuriah ya sanya wa hannu.

Danbazau ya ce gwamnati na taya duk ma’aikatan Nijeriya murna bisa ayyukan da su ke gudanarwa da irin sadaukar da kai da su ka yi wajen aiki tukuru domin ci-gaban Nijeriya.

Ministan, ya kuma yaba wa ma’aikata a kan tabbatar da manufofin gwamnatin tarayya, sannan ya yaba wa kasashen waje bisa kokarin da su ke yi na kawo ayyukan ci-gaba a Nijeriya.

Idan dai ba a manta ba, shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu a kan dokar kara wa ma’aikata albashi zuwa naira dubu talatin daga naira dubu goma sha takwas da ake biya a baya.

Leave a Reply