Home Labaru Kiwon Lafiya Ranar Lafiya: Nijeriya Za Ta Bunkasa Shirin Inshorar Kiwon Lafiya Ta Kasa...

Ranar Lafiya: Nijeriya Za Ta Bunkasa Shirin Inshorar Kiwon Lafiya Ta Kasa – Minista

274
0

Kungiyar Kiwon Lafiya ta Duniya WHO, ta ce za ta cigaba da mara wa gwamnatin Nijeriya baya domin sama wa mutanen ta kiwon lafiya mai nagarta a kan kowa da kowa.

Jami’in kungiyar Rex Mpazange ya sanar da haka, a wajen taron bikin zagayowar ranar Kiwon Lafiya ta Duniya.

Ya ce kungiyar za ta mara wa fannin kiwon lafiya na Nijeriya baya ne, ganin irin namijin kokarin da ta ke yi domin inganta fannin da kuma amincewa da ware wa fannin akalla kashi daya daga cikin kasafin ta na duk shekara.

Mpazange ya kuma yaba wa gwamnati, bisa shirin inshorar lafiya da ta kirkiro domin sama wa mutanen ta kiwon lafiya cikin sauki.

Ministan lafiya Isaac Adewole, ya ce gwamnati ta zage damtse domin inganta asibitocin Nijeriya, a wani mataki na rage yawan zuwa wasu kasashe neman magani.