Fadar Shugaban Kasa Ta Ce Shirye-Sjirye Sun Kammala Domin Gudanar Da Bikin Ranar Dimokuradiyya A Nijeriya.
Jaridar Daily Trust Ta Ruwaito Cewa,Yanzu Ranar 29 Ga Watan Mayu Ta Tashi A Matsayin Ranar Hutu, Yayin Da Aka Maida 12 Ga Watan Yunin Ko Wace Shekara A Matsayin Ranar Hutun Dimokuradiyya, Kuma Buhari Zai Yi Da Wasu Sabbin Nade-Nade Bayan An Kammala Bikin Ranar Dimokuradiyyar.
Idan Dai Ba A Manta Ba, A Litinin Din Da Ta Gabata Ne Shugaba Buhari Ya Rattaba Hannu A Kan Dokar Maida Ranar 12 Ga Watan Yunin Ko Wace Shekara A Matsayin Ranar Hutu A Nijeriya.
Mai Bai Shugaban Kasa Shawara A Kanharkokin Majalisa, Sanata Ita Enang Ya Shaida Haka Ga Manema Labarai A Fadar Shugaban Kasa Da Ke Abuja.
A Na Dai Saran Shugaban Kasa Buhari Zai Bayyana Shirinsa Da Kuma Yadda Wa’adin Mulkin Sa Na Biyu Zai Kasance.
You must log in to post a comment.