Home Labarai Ranar Dimokaradiyya:Tinubu Zai Mika Wa Majalisa Kudirin Mafi Karancin Albashi

Ranar Dimokaradiyya:Tinubu Zai Mika Wa Majalisa Kudirin Mafi Karancin Albashi

9
0
download 2024 06 13T122639.568
download 2024 06 13T122639.568

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya ce gwamnatin sa za ta aike da ƙudiri ga Majalisu Dokokin wanda zai kunshi adadin abin da aka amince da shi ya zama albashi mafi ƙanƙanta ga ma’aikata.

Shugaban kasan wanda ya faɗi haka a yayin jawabin sa ga ƴan Najeriya kan bikin ranar dimukraɗiyya, ya ce lallai yana sane da halin matsin tattalin arzikin da ‘yan najeriyar ke ciki, to sai dai ya nemi ‘yan ƙasa su tallafa wajen cimma dimukraɗiyyar da za ta tabbatar da cigaban tattalin arziki.

Ƴan Najeriya dai sun yi fatan jin ƙarin albashin da suka samu daga bakin shugaban kasa a jawabin nasa na safiyar yau amma hakan bai samu ba.

A ranar Litinin ne dai kwamitin mutum 37 da aka kafa kan albashin mafi ƙanƙanta ya miƙa rahoton sa bayan kwashe kimanin wata biyar da kafa shi.

Wakilan gwamnatin tarayya da na masana’antu masu zaman kansu dai da ke kwamitin na shugaban ƙasa domin tattauna batun albashin sun amince da naira 62,000, inda su kuma wakilan ƙungiyoyin ƙwadago suka kafe a kan naira 250,000.

Leave a Reply