Home Labaru Ramuwar-Gayya: ‘Yan Nijeriya Na Shirin Kaurace Wa Kayan Afirka Ta Kudu

Ramuwar-Gayya: ‘Yan Nijeriya Na Shirin Kaurace Wa Kayan Afirka Ta Kudu

550
0

‘Yan Nijeriya da dama na ci-gaba da ce-ce-ku-ce da kiraye-kiraye a kan kaurace wa amfani da kayayyakin kasar Afirka ta Kudu, sakamakon kin jinin da wasu ‘yan kasar ke nuna wa ‘yan Nijeriya da sauran kasashe mazauna can.

Wasu daga cikin kamfanonin Afirka ta Kudu da ke Nijeriya dai sun hada da kamfanin sadarwa na MTN, da shagunan saye da sayarwa na Shoprite, da kuma kamfanin talabijin na DSTV.

‘Yan Nijeriya musamman a shafukan sada zumunta na yanar gizo, su na nuna bacin ran su a kan yadda kamfanoni mallakar Afrika Ta Kudu ke samun kudi da ‘yan Nijeriya, amma wasu ‘yan kasar ke nuna kin jini da kuma kai hari ga ‘yan Nijeriya mazauna kasar.

Haka kuma, ‘yan Nijeriyar su na amfani da shafukan sada zumunta na Twitter da Facebook, wajen bayyana ra’ayoyin su da kuma kiraye-kirayen a kauracewa kamfanonin kasara Afrika ta Kudu.

Leave a Reply