Home Home Rajistar Sunayen Masu Karɓar Tallafi Ta Ƙasa Ba Sahihiya Ba Ce –...

Rajistar Sunayen Masu Karɓar Tallafi Ta Ƙasa Ba Sahihiya Ba Ce – Gwamnoni

148
0

Majalisar Tsara Tattalin Arziki ta Ƙasa, ta ce Gwamnoni su fito da tsarin cikakkar rajistar marasa galihu, domin wadda Gwamnantin Tarayya ke amfani da ita ba sahihiya ba ce.

Gwamnan Jihar Anambra Charles Soludo ya bayyana haka, jim kadan bayan kammala wani taro da ya gudana a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Gwamna Soludo, ya ce ya dace tallafin da za a fara rabawa ya kasance ya na isa ga marasa galihu, don haka ya kamata su gaya wa kan su gaskiya cewa babu wata sahihiyar rajistar marasa galihu a faɗin Nijeriya.

Charles Soludo, ya ce Gwamnatin Tarayya da Gwamnoni su fito da tsarin tura wa marasa galihu alawus-alawus na rage tsadar rayuwa gwargwadon karfin su.

Ya ce dole su ma Gwamnoni su rage almubazzaranci, domin a halin yanzu babu wani dalilin da gwamna zai fita da tawagar motoci 20.

Leave a Reply