Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Rage Radadi: Tinubu Ya Ba Da Umarnin Ba’Yan Najeriya Tallafi

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin bayar da tallafi domin rage wa ’yan Najeriya radadin cire tallafin mai da Gwamnatin Tarayya ta yi.

Shugaban Kamfanin Mai na Kasa NNPCL Mele Kyari, ya sanar da haka, yana mai cewa biyan tallafin mai da gwamnati ke yi ya zama tarihi, hasali ma ba a ware masa ko sisi ba a kasafin kudi ba.

Da yake bayani bayan ganawar sa da jagororin jam’iyyar APC mai mulki, Kyari ya ce a halin yanzu ma NNPCL na bin gwamnati bashin Naira tiriliyan 2.8 da ya kashe wajen biyan tallafin man, don haka kamfanin ba zai iya ci gaba da biya ba.

Ya ce hasali ma kudin da NNPC ke kashewa wajen biyan tallafin na hana shi sauke nauyin da ya rataya a kan sa, ga shi kasa na bukatar kudaden aiwatar da manyan ayyuka da samar da ababen more rayuwa.

A gefe guda kuma, kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta yi kira ga gwamnatin Najeriya ta dauki matakan da za su hana cire tallafin man jefa ’yan kasa cikin karin matsin rayuwa.


Exit mobile version