Home Labaru Ra’ayi: Shehu Sani Ya Kalubalanci Tazarcen Shugaba Muhammadu Buhari

Ra’ayi: Shehu Sani Ya Kalubalanci Tazarcen Shugaba Muhammadu Buhari

313
0
Ra’ayi: Shehu Sani Ya Kalubalanci Tazarcen Shugaba Muhammadu Buhari
Ra’ayi: Shehu Sani Ya Kalubalanci Tazarcen Shugaba Muhammadu Buhari

Tsohon dan majalisar dattawa Sanata Shehu Sani, ya yi tsokaci game da batun sake zarcewar shugaba Muhammadu Buhari kan karagar mulki da kuma wani kudiri da ke gaban majalisa.

Sanata Shehu Sani dai ya maida martani ne, bayan shugaba Buhari ya tabbatar wa Duniya cewa ba zai sake neman komawa kan mulki a shekara ta 2023 ba.

Sai dai Shehu Sani ya yi gargadin cewa, kada kuma daga baya wani da wani malami ya zo ya na karyar tazarce yin Ubangiji ne.

Tsohon Sanatan, ya kuma yi tsokaci game da kudirin yakar kalaman kiyayya da ke gaban majalisa da ya janyo surutu, inda ya nemi kowa ya fito da ra’ayin sa a fili.

Ya ce ya kamata duk dan majalisar da ba ya tare da kudirin yakar kiyayya ko kuma na takawa dandalin sada zumunta birki ya fito ya yi magana a gaban majalisa bay a yi gum da bakin sa ba.

Leave a Reply