Home Labaru Ra’ayi: Sai An Sauya Fasalin Nijeriya Idan Ana So A Cigaba –...

Ra’ayi: Sai An Sauya Fasalin Nijeriya Idan Ana So A Cigaba – Fayemi

461
0
Kayode Fayemi, Gwamna Jihar Ekiti
Kayode Fayemi, Gwamna Jihar Ekiti

Gwamnan Jihar Ekiti Kayode Fayemi, ya ce sauya fasalin Nijeriya abu ne da dole sai ya faru ko ba-dade ko ba-jima, matukar ana so Nijeriya ta cigaba.

Fayemi ya bayyana haka ne, a lokacin da ya ke gabatar da kasida a wajen wani taro a Cibiyar Jaddada Zaman Lafiya USIP, da ke Birnin Washington DC na kasar Amurka.

‘Yan Najeriya da dama dai sun sha kiraye-kirayen cewa a sauya fasalin Nijeriya, ta yadda za a karkasa wasu bangarorin iko daga tarayya zuwa wasu sassa.

Idan dai za a iya tunawa, a baya mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya goyi bayan sake fasalin Nijeriya, inda har ya bukaci a kirkiro ‘yan sandan jihohi.

Fayemi ya kara da cewa, a cikin Kudirorin Jam’iyyar APC na shekara ta 2015 da 2019, duk akwai batun sake fasalin Nijeriya idan APC ta ci zabe.

Leave a Reply