Home Labaru Ra’ayi Riga: Ooni Na Ife Da Soyinka Sun Ce Masu Kokarin Kafa...

Ra’ayi Riga: Ooni Na Ife Da Soyinka Sun Ce Masu Kokarin Kafa Rugage Marasa Kishin Kasa Ne

365
0

Babban Basaraken Yarabawa Ooni na Ife Adeyeye Ogunwusi da Farfesa Wole Soyinka, sun gargadi manyan ‘yan siyasar kasar nan cewa su dauki matakan da su ka dace wajen yayyafa wa wutar cacar-bakin da ke faruwa a kasar nan ruwan sanyi.

Fitattun manayn Yarabawan biyu sun yi nuni da cewa, a yanzu Nijeriya ba za ta iya juriyar shanye dafin yakin basasa ba kamar yadda ta jure tsakanin shekara ta 1967 zuwa 1970.

Jiga-jigan biyu dai saun bayyna haka a cikin wata sanarwa da su ka sanya wa hannu, jim kadan bayan wani taro da su ka yi a Idi Aba da ke birnin Abeokuta na Jihar Ogun.

Sun kuma yi karin bayani da cewa, irin yadda ake rura wutar kiyayya a tsakanin al’umma, zai iya zama babbar barazana wajen kasancewar Nijeriya kasa daya al’umma daya.

Soyinka da Ooni na Ife, sun bayyana ra’ayoyin su dangane da tsarin da aka nemi shigo da shi na gina wa Fulani rugage a jihohin kasar nan, cewa tsari ne na yi wa jama’a wani salon mulkin mallaka da wasu marasa son ci-gaba ke kokarin tabbatarwa.

Soyinka da Ooni na Ife

Leave a Reply