Home Home Peter Obi Ya Shigar Da Ƙara Don Ƙalubalantar Zaɓen Tinubu

Peter Obi Ya Shigar Da Ƙara Don Ƙalubalantar Zaɓen Tinubu

119
0
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Peter Obi ya shigar da ƙara a hukumance, inda ya ke ƙalubalantar sakamakon zaɓen da ya ba Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC nasara.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Peter Obi ya shigar da ƙara a hukumance, inda ya ke ƙalubalantar sakamakon zaɓen da ya ba Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC nasara.

Peter Obi ya shigar da ƙarar ne a kotun sauraren korafe-korafen zaɓen shugaban ƙasa da ke Abuja.

Hukumar zaɓe dai ta sanar da Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen da aka gudanar, sai dai masu sa ido a kan zaɓen na ciki da wajen Nijeriya sun ce zaɓen ya na cike da kurakurai.

Mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar ta Labour Yunusa Tanko, ya ce a cikin abubuwan da su ke ƙalubalanta akwai rashin cancantar shiga zaɓe na ɗan takarar jam’iyyar APC.

Leave a Reply